(ABNA24.com) Shuwagabanni da gwamnatocin kasashen kungiyar ECOWAS/CEDEAO, na wani taron gaggawa yau Juma’a a Yamai babban birnin Jamhuriya NIjar, domin tattauna halin da ake ciki a kasar Guinea Bissau.
Yayin taron shuwagabannin zasu tattaunawa domin sanin matakin dauka na shawo kan rikicin siyasar kasar ta Guinea Bissau, ta yadda za’a gudanar da sahihin zabe kamar yadda aka tsara a ranar 24 ga watan Nuwamban nan.
Duk da cewa shugaban kasar ta Guinea Bissau, Mario Vaz, baya halartan taron, amma shuwagabannin na fatan shawo kansa nay a mutunta jaddawalin zaben, domin kawo karshen rikicin kasar.
Wasu bayanai na daban sun ce akwai yiyuwar ma kungiyar ta ECOWAS ta dauki mataki akan duk masu kawo tanarki ga zaben kasar ta Guinea, ciki har da shi shugaban kasar Mario Vaz, wanda ya kori firaministansa kwanan baya tare da nada sabuwar gwamnati, lamarin da ya kara dagula rikicin siyasar kasar, kwanaki kadan gabanin zaben kasar.
/129
9 Nuwamba 2019 - 04:33
News ID: 986659

Shuwagabanni da gwamnatocin kasashen kungiyar ECOWAS/CEDEAO, na wani taron gaggawa yau Juma’a a Yamai babban birnin Jamhuriya NIjar, domin tattauna halin da ake ciki a kasar Guinea Bissau.